إعدادات العرض
Ki zauna gwargwadan abinda hailarki take riƙe ki, sannan ki yi wanka
Ki zauna gwargwadan abinda hailarki take riƙe ki, sannan ki yi wanka
Daga Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Cewa Ummu Habiba 'yar Jahsh wacce take ƙarƙashin Abdurrahman Dan Awf ta kawo koken (zubar) jini ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce mata: "Ki zauna gwargwadan abinda hailarki take riƙe ki, sannan ki yi wanka". Ta kasance tana wanka a kowacce sallah.
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Kurdî Português සිංහල Svenska ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá ئۇيغۇرچە Tiếng Việt Kiswahili پښتو অসমীয়া دری Malagasy or Čeština नेपाली Oromoo Română Nederlands Soomaali Кыргызча తెలుగు ไทย Српски മലയാളം Kinyarwanda ಕನ್ನಡ Lietuviųالشرح
Daya daga cikin sahabbai mata ta kawo koken zubar jini (jinin Istihara) zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da take fama da shi, sai ya umarceta ta dakatar da sallah gwargwadan abinda hailarta take tsareta kafin zuubar wannan al'amarin da ya faru da ita, sannan ta yi wanka ta yi sallah, ta kasance tana wanka dan neman lada a kowacce sallah.فوائد الحديث
Jinin cuta (Wato jinin istihala) shi ne: Fitar jini ya zarce ga mace bayan kwanukan hailarta data saba.
Mai jinin cuta tana daukar kanta mai haila gwargwadan kwanukan da haila taka zo mata a cikinsu, kafin abinda ya sameta ya sameta na jinin cuta.
Idan gwargwadan kwanukan al'adarta na asali suka shude, to ita ana daukarta mai tsarki daga al’ada - koda cewa jinin cuta yana tare da ita - sai ta yi wankan daukewar jinin al’ada.
Mai jinin cuta wanka ba ya wajaba akanta a kowacce sallah; domin wankanta - Allah Ya yarda da ita - ya kasance da ijtihadi ne daga gareta, da a ce ya kasance wajibi ne da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana mata shi.
Alwala tana wajaba akan Mai jinin cuta a kowacce sallah; domin hadasinta madawwami ne ba mai yankewa ba ne, misalinta dukkan wanda karinsa madawwami ne kamar wanda a tare da shi akwai yoyon fitsari, ko fitar tusa mai a koyaushe.
Tambayar ma'abota ilimi daga abinda yake rikitarwa a al'amuran Addini, yayin da wannan matar ta kawo kuka ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ta tambaye shi game da yawan jinin da yake samunta.
التصنيفات
Haila da Nifasi da jinin cuta