Canfi shirka ne, canfi shirka ne, canfi shirka ne, - sau uku -", babu wani a cikinmu saidai, saidai cewa Allah - Mai girma da daukaka - Yana tafiyar da shi da dogara (ga Allah)

Canfi shirka ne, canfi shirka ne, canfi shirka ne, - sau uku -", babu wani a cikinmu saidai, saidai cewa Allah - Mai girma da daukaka - Yana tafiyar da shi da dogara (ga Allah)

Daga Abdullahi Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agar shi - ya ce: "Canfi shirka ne, canfi shirka ne, canfi shirka ne, - sau uku -", babu wani a cikinmu saidai, saidai cewa Allah - Mai girma da daukaka - Yana tafiyar da shi da dogara (ga Allah).

[Ingantacce ne] [Ibnu Majah ne ya Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargadi daga canfi shi ne canfi daga kowanne abu, abin ji ne ko abin gani, daga tsuntsayene ko dabbobi ko masu larurori ko lambobi ko kwanuka ko makamancin hakan, kadai ya ambaci canfi ne domin cewa shi ne ya fi shahara a lokacin Jahiliyya, asalinsa shi ne sakin tsuntsu a lokacin fara wani aiki na tafiya ne ko kasuwanci ko makamancin hakan, idan ya tashi a bangaren dama sai ya yi yunkuri ya ci gaba da abinda yake nufi, idan ya tashi bangaren hagu sai ya canfa ya kame daga abinda yake nufi. Ya bada labarin cewa hakan shirka ce, kadai canfi ya zama shirka; domin ba mai zuwa da alheri sai Allah, kuma ba mai tunkude sharri sai Allah Shi kadai ba shi da abokin tarayya. Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ambaci cewa wani abu na canfi zai iya darsuwa a zuciyar musulmi, saidai ya wajaba akansa ya tunkude shi da dogaro ga Allah, tare da aikata sabubba.

فوائد الحديث

Canfi shirka ne; domin acikinsa akwai rataya zuciya da wanin Allah.

Muhimmancin maimaita mas'aloli muhimmai, dan a kiyaye su kuma su tabbata a cikin zukata.

Dogaro ga Allah - Madaukain sarki - yana tafiyar da canfi.

Umarni da dogaro ga Allah Shi kadai, da rataya zuciya da Shi - tsarki ya tabbatar maSa -.

التصنيفات

Shirka, Shirka, Falalar Ayyukan Zukata, Falalar Ayyukan Zukata