Ya kai baffana, ka ce : Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kalma ce wacce zan kafa maka hujja da ita awurin Allah

Ya kai baffana, ka ce : Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kalma ce wacce zan kafa maka hujja da ita awurin Allah

Daga Sa'id Dan Musayyib daga babansa ya ce: Lokacin da mutuwa ta zo wa Abu Dalib, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo masa sai ya samu Abu jahal da Abdullahi Dan Abu Umayyah Dan Mugira a wurrinsa, sai ya ce: "Ya kai baffana, ka ce : Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kalma ce wacce zan kafa maka hujja da ita awurin Allah", sai Abu jahal da Abdullahi dan Abu Umayyah suka ce : Kana kin tafarkin Abdul Muddalib, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai gushe ba yana bijiro masa da ita, suma suna maimaita masa waccan maganar, har Abu Dalib ya ce karshen abinda ya fada musu: Akan tafarkin Abdul Muddalib ya ki fadar: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wallahi zan nemamaka gafara muddin ba'a hanani ba". Sai Allah yaYa saukar da: {Bai kasance ga Annabi ba da wadanda suka yi imani da su nema wa mushrikai gafara ba} [Al-Taubah: 113], kuma Alllah Ya saukar asha'anin Abu Dalib, sai Ya cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: {Lallai kai ba zaka shiryar da wanda kake so ba sai dai Allah Yana shiryar da wanda Ya so} [Al-Kasas: 56].

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiga wurin baffansa Abu Dalib alhali shi yana kan gargara, sai ya ce masa: Ya baffana, ka ce : "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, wata kalmace da zan yi maka shaida da ita a wurin Allah, sai Abu Jahal da Abdullahi Dan Abu Umayya suka ce: Ya Abu Dalib, zaka bar tafarkin babanka Abdul Muddalib?! Shi ne bautar gumaka, basu gushe ba suna yi masa magana har ya fadi karshen wani abinda ya zantar da su da shi: Akan tafarkin Abdul Muddalib, tafarkin shirka da bautar gumaka, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Zan roka maka gafara muddin Ubangijina bai hanani hakan ba, sai fadin Allah - Madaukakin sarki - ya sauka: {Bã ya kasancẽwa ga Annabi da waɗanda suka yi ĩmãni, su yi istigifãri ga mushirikai, kuma kõ dã sun kasance ma'abũta zumunta ne daga bãyan sun bayyana a gare su, cẽwa lalle ne, sũ, 'yan Jahĩm ne} [Al-Taubah: 113], kuma fadin Allah - Madaukakin sarki - ya sauka a sha'anin Abu Dalib: {Lalle ne kai bã ka shiryar da wanda ka so, amma kuma Allah Yanã shiryar da wanda Yake so, kuma Shi ne Mafi sani daga mãsu shiryuwa} [Al-kasas: 56], lallai cewa kai ba ka shiryar da wanda ka so shiriyarsa, kawai kai isarwa ce taka, Allah Yana shiryar da wanda yake so.

فوائد الحديث

Haramcin nemawa mushrikai gafara, duk yadda kusancinsu ya kasance da ayyukan su da kyautatawarsu.

Koyi da iyaye da manya akan shirka yana daga aikin 'yan Jahiliyya.

Cikar tausayin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kwadayinsa akan kiran mutane da shiriyarsu.

Raddi ga wanda ya yi da'awar musuluntar Abu Dalib.

Ayyuka da cikawa ne.

Bacin rataya ga Annabi - tsira da aminci su tabbata agare shi - da waninsa dan jawo amfani ko tunkude cuta.

Wanda ya ce: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah" akan ilimi da yakini da kudircewa ya shiga Musulunci.

Cutarwar munanan mutane da abokanan sharri ga mutum.

Ma'anar "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah": Barin bautar gumaka da waliyyai da mutanen kirki, da kadaita Allah da bauta, kuma cewa mushrikai suna sanin ma'anarta.

Halaccin gaishe da mara lafiya mushriki idan ana kwadayin musuluntarsa.

Shiriya ta gamda -katar tana hannun Allah ne Shi kadai ba Shi da abokin tarayya, kawai shiriya ta nuni da shiryarwa da isarwa tana ga Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

التصنيفات

Tafsirin Al-qur’ani, Kira zuwa ga Allah