Idan ɗayanku ya haɗu da ɗan uwansa to ya yi masa sallama, idan bishiya ko katanga ko dutse ya tsare tsakaninsu sannan ya haɗu da shi to ya yi masa sallama kuma

Idan ɗayanku ya haɗu da ɗan uwansa to ya yi masa sallama, idan bishiya ko katanga ko dutse ya tsare tsakaninsu sannan ya haɗu da shi to ya yi masa sallama kuma

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce : "Idan ɗayanku ya haɗu da ɗan uwansa to ya yi masa sallama, idan bishiya ko katanga ko dutse ya tsare tsakaninsu sannan ya haɗu da shi to ya yi masa sallama kuma".

[Ingantacce ne] [Abu Daud Ya Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kwaɗaitar da musulmi da yin sallama ga ɗan uwansa musulmi duk lokacin da ya haɗu da shi, koda sun kasance suna tafiya tare ne kuma wani abu mai rabawa ya raba su, kamar bishiya ko gini ko babban dutse, sannan ya haɗu da shi bayan nan to ya yi masa sallama karo na biyu.

فوائد الحديث

An so yaɗa sallama, kuma a maimaitata a lokacin canjin hali.

Tsananin kwaɗayinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan yaɗa sunnar sallama da kai matuƙa a cikinta; dan abinda ke cikinta na jawo soyayya da hada tsakanin musulmai.

Sallama ita ce faɗin: Assalamu alaikum, (Aminci ya tabbata a gareku) ko: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh, wato(Aminci ya tabbata a gareku da rahamar Allah da albarkarSa), banda musafahar da take faruwa alokacin farkon haɗuwa.

Sallama addu'a ce, musulmai suna cikin buƙatuwar junansu su yi wa junansu addu'a koda hakan ya maimaitu.

التصنيفات

Ladaban Sallama da Neman izini