إعدادات العرض
Ka shiryar da ni ga wani aiki wanda idan na yi shi, zan shiga aljanna, ya ce: "Ka bauta wa Allah, kada ka hada Shi da komai, ka tsayar da sallah, ka bayar da zakkar da aka wajabta, ka azimci Ramadan
Ka shiryar da ni ga wani aiki wanda idan na yi shi, zan shiga aljanna, ya ce: "Ka bauta wa Allah, kada ka hada Shi da komai, ka tsayar da sallah, ka bayar da zakkar da aka wajabta, ka azimci Ramadan
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Cewa wani balaraben kauye ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Ka shiryar da ni ga wani aiki wanda idan na yi shi, zan shiga aljanna, ya ce: "Ka bauta wa Allah, kada ka hada Shi da komai, ka tsayar da sallah, ka bayar da zakkar da aka wajabta, ka azimci Ramadan" Ya ce: Na rantse da Wanda raina yake a hannunSa, ba zan yi kari akan wannan ba, lokacin da ya juya ya tafi sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Wanda yake son ya kalli wani mutum daga 'yan aljanna, to ya yi duba zuwa ga wannan".
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Kurdî Kiswahili Português සිංහල Svenska ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá ئۇيغۇرچە Tiếng Việt پښتو অসমীয়া دری Кыргызча or Malagasy नेपाली Čeština Oromoo Română Nederlands Soomaali తెలుగు മലയാളം ไทย Српски Kinyarwanda ಕನ್ನಡ Lietuvių Shqipالشرح
Wani mutum ya gabato daga mutanen kauye ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - dan ya nuna masa aikin da zai shigar da shi aljanna, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya amsa masa da cewa shiga aljanna da tsira daga wuta sun tsaya akan bada rukunan Musulunci, na bautar Allah Shi kadai, kuma kada ka hada wani abu da Shi. Ka tsaida salloli biyar din Allah Ya wajabta su akan bayinSa a kowanne yini da dare. Ka bada zakkar dukiyar da Allah Ya wajabtasu akanka, ka bada su ga wadanda suka cancanta l. Ka kuma kiyaye akan azimin watan Ramadan a lokacinsa. Sai mutumin ya ce na rantse da wanda raina yake a hannunSa ba zan kara komai akan aikin da aka wajabta ba wanda na ji shi daga gareka na ayyukan da'a ba, kuma ba zan rage ba daga garesu ba. Lokacin da ya juya (ya tafi) sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Wanda yake son ya yi duba zuwa ga wani mutum daga 'yan aljanna to ya yi duba zuwa ga wannan balaraben kauyen.فوائد الحديث
Kadaita Allah - Madaukakin sarki - da ibada shi ne farkon abinda ake farawa da shi a kira zuwa ga Allah.
Takaituwa da koyar da wajibai ga wanda ya zama farkon shiga Musulunci.
Kira zuwa ga Allah - Madaukakin sarki - babu makawa daga bi a sannu a sannu.
Kwadayin mutumin akan neman sanin al'amarin Addininsa
Idan musulmi ya takaita akan wajibai to cewa shi ya tsira, saidai anan ba ya nufin sakaci ga nafilifili; domin nafila ana cike tawayar farilla da ita.
Kebance wasu daga ibadu da ambato dalili ne akan muhimmancinsu da kwadaitarwa akan su, (hakan) ba ya nufin rashin wajabcin waninta.
التصنيفات
Ladaban Malami da Xalibi