Duk al'ummata an yafe musu sai masu bayyanarwa

Duk al'ummata an yafe musu sai masu bayyanarwa

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Duk al'ummata an yafe musu sai masu bayyanarwa, kuma yana daga bayyanarwa mutum ya aikata wani aiki (mummuna) da daddare, sannan ya wayi gari Allah Ya rufa masa asiri, sai ya ce: Ya (ya falalarsa kansa) wane, jiya da daddare na aikata kaza da kaza, alhali ya kwana Uabangijinsa Ya rufa masa asiri, shi kuma ya wayi gari yana tona asirin da Allah Ya rufa masa".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa musulmi mai laifi ana yi masa kwadayin afuwar Allah da gafararSa, sai mai bayyanar da sabo dan alfahari da rashin kunya, to ba ya cancantar afuwa; ta inda yake aikata laifi da daddare, sannan ya wayi gari alhali Allah Ya rufa masa asiri, sai ya zantar da waninsa da cewa shi ya aikata sabo kaza jiya, ya kwana Ubangijinsa Ya rufa masa asiri, shi kuma ya wayi gari yana tona asirin da Allah Ya rufa masa!!

فوائد الحديث

Munin bayyanar da sabo bayan rufa asirin Allah - Madaukakin sarki - ya yi a gare shi .

A bayyanar da sabo akwai yayata alfasha tsakanin muminai.

Wanda Allah Ya rufa masa asiri a duniya Zai rufa masa asiri a lahira, wannan yana daga yalwar rahamar Allah - Madaukakin sarki - ga bayinSa.

Wanda aka jarraba da wani sabo to ya wajaba ya rufawa kansa asiri kuma ya tubarwa Allah.

Girman zunubin masu bayyanarwa wadanda suke nufin bayyanar da sabo, kuma suna barin afuwar Allah taba wuce su.

التصنيفات

Zargin Savo