Wanda ke kan abin hawa shi ke sallama ga mai tafiya, mai tafiya kuma yana sallama ga wanda ke zaune, kadan kuma (suna sallama) ga masu yawa

Wanda ke kan abin hawa shi ke sallama ga mai tafiya, mai tafiya kuma yana sallama ga wanda ke zaune, kadan kuma (suna sallama) ga masu yawa

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ke kan abin hawa shi ke sallama ga mai tafiya, mai tafiya kuma yana sallama ga wanda ke zaune, kadan kuma (suna sallama) ga masu yawa".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana shiryarwa ga ladabin yin gaisuwar Musulunci tsakanin mutane "Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarsa", Sai karami ya yi sallama ga babba, wanda ke kan abin hawa ga mai tafiya a kasa, mai tafiya a kasa ga wanda ke zaune, adadi kadan ga adadi mai yawa.

فوائد الحديث

An so sallama akan abinda Hadisi ya zo da shi, idan mai tafiya a kasa ya yi sallama ga wanda ke kan abin hawa da makamancin hakan daga abinda aka ambata, to ya halatta, sai dai cewa shi sabanin abinda yafi ne.

Yada sallama akan siffar da ta zo a cikin Hadisi yana daga sabubban soyayya da kauna.

Idan sun kasance daidai a cikin abinda aka ambata, to mafificinsu shi ne wanda ya fara sallama.

Cikar wannan shari'ar a cikin bayanin dukkan abinda mutane suke bukatarsa.

koyar da ladubban sallama da bawa kowanne mai hakki hakkinsa.

التصنيفات

Ladaban Sallama da Neman izini