Shin kuna ganin cewa da ace akwai wata korama a kofar dayanku yana wanka a cikinta kowacce rana sau biyar, shin kuna zatan wani abu na dattinsa zai rage ?

Shin kuna ganin cewa da ace akwai wata korama a kofar dayanku yana wanka a cikinta kowacce rana sau biyar, shin kuna zatan wani abu na dattinsa zai rage ?

Daga Abu Huraira Allah ya yarda da shi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Shin kuna ganin cewa da ace akwai wata korama a kofar dayanku yana wanka a cikinta kowacce rana sau biyar, shin kuna zatan wani abu na dattinsa zai rage ?" Suka ce: Ba abin da zai rage dattinsa, ya ce: "To hakan tamkar salloli biyar ne, Allah Yana shafe kurakurai da su".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kamanta salloli biyar a kowanne yini da dare a kawarwa da kankarewarsu ga kananan zunubai da kurakurai da korama a kofar mutum da yake wanka a cikinta kowacce rana sau biyar, babu wani abu da zai ragu daga dattinsa.

فوائد الحديث

Wannan falalar ta kebanci kankare kananun zunubai ne, amma manya babu makawa daga tuba daga gare su.

Falalar yin salloli biyar da kiyayewa akansu da sharuddansu da rukunansu da wajibansu da sunnoninsu.

التصنيفات

Falalar Sallah