ku umarci 'ya'yanku da yin sallah alhali su suna 'yan shekara bakwai, kuma ku dake su akanta alhali su suna 'yan shekara goma, kuma ku raba tsakaninsu a wurin kwanciya

ku umarci 'ya'yanku da yin sallah alhali su suna 'yan shekara bakwai, kuma ku dake su akanta alhali su suna 'yan shekara goma, kuma ku raba tsakaninsu a wurin kwanciya

Daga Amr Dan Shu'aib daga babansa daga kakansa ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "ku umarci 'ya'yanku da yin sallah alhali su suna 'yan shekara bakwai, kuma ku dake su akanta alhali su suna 'yan shekara goma, kuma ku raba tsakaninsu a wurin kwanciya".

[Ingantacce ne] [Al-Tirmithi Ya Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa ya wajaba akan uba ya umarci 'ya'yansa - maza da mata - da yin sallah alhali suna da shekara bakwai, kuma ya sanar dasu abinda suke bukata dan tsaida ita. Idan suka kai shekara goma sai ya yi kari akan umarnin, sai ya yi duka akan kasa yin Sallar, kuma ya raba a tsakaninsu a shinfida.

فوائد الحديث

Sanar da 'ya'ya kanana al'amuran Addini kafin balaga, daga mafi muhimmancinsu sallah.

Duka yana kasancewa ne dan ladabtarwa, ba dan azabtarwa ba, sai ya yi dukan da ya dace da halinsa.

Kulawar shari'a a kiyaye mutunci, da toshe kowacce hanyar da zata iya kaiwa zuwa barna.

التصنيفات

Wajabcin Sallah da Hukuncin wanda ya barta