Wanda ya sallaci sallar Asuba, to, zai kasance cikin alƙawarin Allah

Wanda ya sallaci sallar Asuba, to, zai kasance cikin alƙawarin Allah

Daga Jundub ɗan Abbdullah AL Qasri- Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon - Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Wanda ya sallaci sallar Asuba, to, zai kasance cikin alƙawarin Allah, Kada ku kuskura Allah Ya kamaku da wani (laifi) cikin alƙawarinsa; domin cewa duk wanda ya nemeshi da wani abu (na laifi) Zai kamashi, sannan Ya kifar da shi ta fuskarsa a cikin wutar Jahannama".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa wanda ya sallaci Asuba, to, zai kasance cikin kiyayewar Allah da gadinsa da tsarinsa, kuma Zai yi kariya gareshi, kuma zai yi ɗauki gareshi. Sannan (Annabi) tsira da aminci su tabbata a gareshi ya yi gargaɗi game da warware wannan alƙawarin da ɓatashi, ko dai da barin sallar Asuba, ko da bijirowa mai sallatarta da ta'addanci a kansa, to, duk wanda ya aikata haka to haƙiƙa ya keta wannan tsarin, kuma ya cancanci narko mai tsanani na cewa Allah Zai nemeshi saboda abin da ya yi sakaci na haƙƙinsa, wanda kuwa Allah Ya nemeshi Zai kamashi, sannan Ya jefashi a wuta ta fuskarsa.

فوائد الحديث

Bayanin muhimmancin (sallar) Asuba da falalarta.

Gargaɗi mai tsanani game da bijirowa da mummunan (aiki) ga wanda ya sallaci Asuba.

Kamun Allah - Maɗaukakin sarki - ga wanda yake bijirowa bayinsa na gari.

التصنيفات

Falalar Sallah, Falalar Sallah