Imani tsagi saba’in- ko Sittin- da wani abu ne, mafi falalarsu faɗin: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, mafi ƙasa kuma kawar da ƙazanta daga hanya

Imani tsagi saba’in- ko Sittin- da wani abu ne, mafi falalarsu faɗin: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, mafi ƙasa kuma kawar da ƙazanta daga hanya

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Imani tsagi saba’in- ko Sittin- da wani abu ne, mafi falalarsu faɗin: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, mafi ƙasa kuma kawar da ƙazanta daga hanya. Kunya wani tsagi ce na imani.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayyana cewar imani rassa ne, kuma halaye ne masu yawa, sun kunshi ayyuka da ƙudurce-ƙudurcen zuciya da maganganu. Kuma mafi girman ɗabi’un imani da falala shi ne faɗin: "Babu abin bautawa da cancanta sai Allah". Tare da sanin ma’anarta, da kuma aiki da abin da take nunawa na cewa Allah Shi ne abin bauta guda ɗaya, wanda Ya cancanci a bauta masa Shi kaɗai ban da wani ba shi ba. Kuma mafi ƙarancin ayyukan imani shi ne kawar da duk abin da zai cutar da mutane a kan hanyoyi. Sannan sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ba da bayanin cewa kunya tana cikin ɗabi’u na imani, kuma ɗabi’a ce da take zaburarwa a kan yin abu mai kyau da kuma barin mummuna.

فوائد الحديث

Imani matakai ne, wani sashin nasu ya fi wani falala.

Imani kuma magana ce da kuma aiki da ƙudurin zuci

Jin kunyar Allah maɗaukaki yana sanyawa kada ya ganka a inda ya hanaka, kada kuma ya rasaka a inda ya umarceka.

Anbaton adadi ba ya nuna iyakarsu kenan, sai dai yana nuna yawan ayyukan imani ne, domin Larabawa su kan ambaci abu da adadi ba tare da suna nufin kore abin da ba shi ba.

التصنيفات

Qaruwar Imani da Raguwarsa