sun kasance suna koyan ayoyi goma daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ba sa koyan wasu goman daban har sai sun san abinda ke cikin wadannan na ilimi da aiki

sun kasance suna koyan ayoyi goma daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ba sa koyan wasu goman daban har sai sun san abinda ke cikin wadannan na ilimi da aiki

Daga Abu Abdurrahman Al-Sulami - Allah ya yi masa rahama - ya ce: Wadanda suka kasance suna karantar damu daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sun zantar damu cewa su sun kasance suna koyan ayoyi goma daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ba sa koyan wasu goman daban har sai sun san abinda ke cikin wadannan na ilimi da aiki, suka ce: Sai muka koyi ilimi da aiki.

[Hasan ne] [Ahmad ne ya rawaito shi]

الشرح

Sahabbai - Allah Ya yarda da su - sun kasance suna koyo daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ayoyi goma daga Alkur’ani, ba sa cirata zuwa wasu har sai sun san abinda ke cikin wadannan goman na ilimi kuma suna aiki da shi, sai suka koyi ilimi da aiki gaba daya.

فوائد الحديث

Falalar sahabbai - Allah Ya yarda da su - da kwadayinsu akan koyon Alkur’ani .

Koyon Alkur’ani yana kasancewa ne da ilimi da aiki da abinda ke cikinsa, ba kawai da karanta shi da kuma hardace shi ba kawai.

Ilimi yana kasancewa ne kafin fada da aikatawa .

التصنيفات

Ilimin Tajweedi, Ladaban Karanta Al-qur’ani da kuma Haddace shi, Falalar Ilimi