Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsinewa namijin da ya sanya kayan mace, da macen da ta sanya kayan namiji

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsinewa namijin da ya sanya kayan mace, da macen da ta sanya kayan namiji

Daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsinewa namijin da ya sanya kayan mace, da macen da ta sanya kayan namiji.

[Ingantacce ne]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi addu'a da korewa da nisantarwa daga rahamar Allah ga dukkan namijin da ya yi kama da mace a cikin tufafin da suka keɓanci mata; daidai ne a cikin kama ne ko launi ko kaifiyya ko hanyar sanyawa da ado ko wanin haka. Ko mace ta yi kama da kayan da suka keɓanci maza kamar haka, kuma shi laifi ne babba daga manyan laifuka.

فوائد الحديث

AlShaukani ya ce: Haramcin kamanceceniyar mata da maza da maza da mata; domin cewa tsinuwa ba ta kasancewa sai akan aikata haram.

Ibnu Usaimin ya ce: Abinda ya kasance abin tarayya ne tsakaninsu misalin sashin fanilolin da maza da mata suke sanyawa to cewa wannan babu laifi da shi, wato babu laifi maza da mata su ɗaura su; domin cewa shi sun yi tarayya ne.

التصنيفات

Kamanceceniyar da aka Haramta, Kaya da kuma Ado