Yana daga mafi girman jihadi kalmar adalci a a gaban azzalumin sarki

Yana daga mafi girman jihadi kalmar adalci a a gaban azzalumin sarki

Daga Abu sa'id AlKhudri - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Yana daga mafi girman jihadi kalmar adalci a a gaban azzalumin sarki".

[Hasan ne ta wani Sanadin]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa daga mafi girma da anfanin nau'ikan jihadi a tafarkin Allah - Madaukakin sarki - shi ne kalma ta adalci da gaskiya a wurin azzalumin sarki (shugaba); domin cewa shi aiki ne da alama ce ta horo da aikin alheri da hani daga mummuna, daidai ne ya kasance da fada ne ko rubutu ko aikatawa ko wanin hakan wanda maslaha zata tabbata da shi kuma barna ta tunkude barna.

فوائد الحديث

Horo da aikin alheri da hani daga mummuna yana cikin jihadi.

Yi wa shugaba nasiha yana daga mafi girman jihadi, sai dai yana wajaba ya zama da ilimi da hikima da kuma tabbatarwa.

AlKhaɗɗabi ya ce: Kaɗai hakan ya zama mafificin jihadi; domin wanda ya yaki makiyi ya kasance mai kaikawo tsakanin kwaɗayi da tsoro bai sani ba shin zai yi rinjaye ne ko za'a rinjaye shi, shi kuma mai yi wa shugaba nasiha abin rinjaya ne a hannunsa idan ya faɗi gaskiya kuma ya umarce shi da aikin alheri to hakika ya bijiro da salwantar da rayuwar sa, kuma ya kai kansa ga halaka, sai hakan ya zama mafificin nau’ukan jihadi saboda rinjayar da tsoro, an ce: Kaɗai hakan ya zama mafificin jihadi ne; domin shugaba da ya karbi maganarsa da anfanin ya game adadi mai yawa na mutane sai maslaha ta tabbata.

التصنيفات

Falalar Umarni da kyakkyawan aiki da hani da Mummuna