Duk wanda ya shirya mayaki a tafarkin Allah to hakika ya yi yaki, wanda ya maye gurbin wani mayaki a tafarkin Allah (a gidansa) da alheri to hakika ya yi yaki

Duk wanda ya shirya mayaki a tafarkin Allah to hakika ya yi yaki, wanda ya maye gurbin wani mayaki a tafarkin Allah (a gidansa) da alheri to hakika ya yi yaki

Daga Zaid ɗan Khalid - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Duk wanda ya shirya mayaki a tafarkin Allah to hakika ya yi yaki, wanda ya maye gurbin wani mayaki a tafarkin Allah (a gidansa) da alheri to hakika ya yi yaki".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya tanadarwa wani mayaki a tafarkin Allah sabubban tafiyarsa da abinda yake bukatuwa gare shi daga abinda babu makawa gare shi na makami da abin hawa, da abinci, da ciyarwa da waninsu; to shi yana cikin hukuncin mai yin yaki, kuma ladan mayaki zai same shi . wanda ya jibinci al'amarin mayaki da alheri, kuma ya maye gurbinsa a cikin kula da iyalansa a lokacin da ba ya nan to shi yana cikin hukuncin mayaki yake.

فوائد الحديث

Kwaɗaitar da musulmai akan taimakekeniya akan ayyukan alheri.

Ibnu Hajar ya ce: A cikin wannan Hadisin a kwai kwaɗaitarwa akan kyautatawa ga wanda ya aikata wata maslaha ga musulmai, ko ya tsaya da wani al'amari daga abubuwan da ya shafesu.

Ka'ida gamammiya: Cewa wanda ya taimaki wani mutum a cikin aikin ɗa'a daga ayyukan ɗa'a ga Allah to yana da kwatankwacin ladansa, ba tare da an rage wani abu daga ladansa ba.

التصنيفات

Falalar Jahadi