An umurce ni da in yaki mutane har sai sun shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma (Annabi) Muhammadu Manzon Allah ne, su tsaida sallah, su bayar da zakka

An umurce ni da in yaki mutane har sai sun shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma (Annabi) Muhammadu Manzon Allah ne, su tsaida sallah, su bayar da zakka

Daga Dan Umar - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "An umurce ni da in yaki mutane har sai sun shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma (Annabi) Muhammadu Manzon Allah ne, su tsaida sallah, su bayar da zakka, idan suka aikata hakan sun tsare jinanensu da dukiyoyinsu daga gareni sai dai da hakkin Musulunci, kuma hisabinsu yana ga Allah".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa Allah Ya umarce shi da yakar mushrikai har sai sun shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai ba Shi da abokin tarayya, kuma su shaida manzanci ga (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, da aiki da abinda wannan shaidar ta hukunta na kiyayewa akan salloli biyar a yini da dare, kuma su bada zakka ta wajibi ga wadanda suka cancanta. Idan suka aikata wadannan al'amuran to Musulunci ya tsare jinanensu da dukiyoyinsu, kashe su ba ya halatta sai dai idan sun aikata laifi ko wata barnar da za su cancanci kisa akanta, ta hanyar wajabcin hukunce-hukuncen Musulunci, sannan ranar AlKiyama Allah - Madaukakin sarki - Zai jibinci hisabunsu inda Yake sanin sirrikansu.

فوائد الحديث

Hukunce-hukunce kawai suna gudana ne akan zahiri, Allah ne Yake jibintar sirrika.

Muhimmanci kira zuwa Tauhidi kuma cewa shi ne farkon abinda za'a fara da shi a Da'awa.

Wannan Hadisin ba ya nufin tilasta mushrikai kan shiga Musulunci, kai su wadanda aka bai wa zabi ne tsakanin shiga Musulunci ko bada jizya, idan suka ki, sai hana kira zuwa ga Musulunci, to babu makwa sai yaki ta hanyar dokokin hukunce-hukuncen Musulunci.

التصنيفات

Abubuwan da suke warware Musulunci