إعدادات العرض
Shayarwa tana haramta dukkan abin da haihuwa take haramtawa
Shayarwa tana haramta dukkan abin da haihuwa take haramtawa
Daga Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a greshi - ya ce: «Shayarwa tana haramta dukkan abin da haihuwa take haramtawa».
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी ئۇيغۇرچە Kurdî Português සිංහල دری অসমীয়া پښتو O‘zbek Tiếng Việt Македонски Kiswahili ភាសាខ្មែរ ਪੰਜਾਬੀ తెలుగు ไทย Moore አማርኛ Magyar Azərbaycan ქართული ಕನ್ನಡ ગુજરાતી Українська Shqip Кыргызча Kinyarwanda Српски тоҷикӣ Wolof Čeština தமிழ் नेपाली മലയാളം kmr ms Lietuvių Deutschالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa duk abin da haihuwa da nasaba suke haramtawa na yakumbo (Inna) ce ko baffa ko ɗan uwa...to shayarwa tana haramta shi, kuma shayarwa tana halatta abin da haihuwa take halattawa na hukunce-hukunce.فوائد الحديث
Hadisin ƙa'idace a cikin huknce-hukuncen shayarwa.
Ibnu Hajar ya ce: Faɗinsa: (Shayarwa tana haramta abin da haihuwa take haramtawa) wato: Kuma tana halatta abin da take halattawa, shi ne a ijma'i a kan abin da yake rataye da haramcin aure da abubuwan da ke biye da shi, da yaɗuwar haramci tsakanin wanda aka shayar da kuma 'ya'yan mai shayarwar, da saukar da su a matsayin 'yan'uwa a cikin halaccin kallo da kaɗaitaka da tafiya. Saidai ragowar hukunce-hukunen 'yan uwantaka ba ya hawa a kansa na gado tsakani da wajabcin ciyarwa da 'yantawa ta hanyar mallaka da shaida da diyya da kuma sarayar da ƙisasi.
Tabbatar da hukuncin haramci na har abada ta hanyar shayarwa.
Wasu hadisan daban, sun yi nuni akan cewa haramci ta hanyar shayarwa yana tabbata ne da shayarwa biyar sanannu, kuma su zama a cikin shekara biyun farko (na wanda aka shayar ɗin).
Waɗanda suka haramta ta hanyar nasaba su ne: Iyaye mata, kakanni mata suna shiga ciki, ko da kakannin kakanni ne ta ɓangaren uwa da uba.
Da 'ya'ya mata: 'Ya'yan 'ya'ya mata suna shiga ciki, da 'ya'yan 'ya'ya ko sunyi nisa. Da 'yan uwa mata: Duk ɗaya ne shin sun kasance ta ɓangaren uba da uwa ne, ko ta ɓangaren ɗayansu. Da baffannai: Kuma dukkanin 'yan uwan uba shaƙiƙai da waɗanda ba shaƙiƙaiba suna shiga ciki, haka nan dukkanin 'yan uwan kakanninka, ko da sun yi nisa. Da yakumbai: Kuma dukkanin 'yan uwan uwa shaƙiƙai da wasunsu suna shiga ciki, haka nan dukkanin 'yan uwan kakanni, ko da sun yi nisa, duk ɗaya ne shin sun kasance ne kakanni ta ɓangaren uba ko ta ɓangaren uwa, da 'ya'yan ɗan uwa, da 'ya'yan 'yar uwa, da 'ya'yansu suna shiga cikinsu ko da sun yi nisa.
Waɗanda suka haramta da shayarwa, dan haka duk abin da yake haramta saboda nasaba to yana haramta saboda shayarwa, duk matar da ta haramta saboda nasaba to kwatankwacinta ta haramta saboda shayarwa, sai uwar ɗan uwansa da 'yar uwar ɗansa daga shayarwa to bata haramta.
التصنيفات
Shayarwa