إعدادات العرض
Idan kun ga shi to ku yi azimi, idan kun gan shi ku busha ruwa, idan an ɓoye muku (shi) to ku kaddara (kwanakinsa) sa
Idan kun ga shi to ku yi azimi, idan kun gan shi ku busha ruwa, idan an ɓoye muku (shi) to ku kaddara (kwanakinsa) sa
Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Idan kun ga shi to ku yi azimi, idan kun gan shi ku busha ruwa, idan an ɓoye muku (shi) to ku kaddara (kwanakinsa) sa".
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी ئۇيغۇرچە Português Kurdî සිංහල Nederlands অসমীয়া Tiếng Việt Kiswahili ગુજરાતી پښتو አማርኛ Oromoo ไทย Română മലയാളംالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana alamar shigar watan Ramadan da kuma fitarsa, sai ya ce: Idan kun ga injirin watan Ramadan to ku azimce shi, idan girgije ya tsare tsakaninku da shi ya ɓuya gareku; to ku ƙirga kwanaki talatin na watan Sha'aban, idan kun ga jinjirin watan Shawwal to ku ajiye azumi, idan girgije ya tsare tsakaninku da shi ya ɓuya gareku; to ku ƙirga kwana talatin ga watan Ramadan.فوائد الحديث
Dogara a tabbatar da shigar wata akan gani ne ba akan lissafi ba.
Ibunl Munzir ya cirato ijma'i akan cewa azimi ba ya wajaba idan shigar watan Ramadan ya kasance da lissafi ne kawai ba ganin (wata) ba.
Wajabcin cika Sha'aban kwana talatin idan girgije ko makancinsa ya tsare ganin jinjirin watan Ramadan.
Watan sama ba ya kasancewa sai kwana ashirin da tara, ko kwanaki talatin.
Wajabcin cika Ramadan kwanaki talatin idan girgije ko waninsa ya tsare (ganin) jinjirin watan Shawwal.
Wanda yake a wurin da babu wanda yake bibiyar al'amarin musulmai a sha'anin azimi, ko akwai wanda bai kula da hakan ba to yana kamata ya kiyaye hakan ya bibiye shi da wanda hakan yake tabbata a wurinsa da ganin kansa ko da ganin wanda ya aminta da shi; sai ya yi azimi da hakan kuma yasha ruwa.
التصنيفات
Ganin Wata