Dukkaninku masu kiwone to abin tambayane daga abinda yake kiwonta,

Dukkaninku masu kiwone to abin tambayane daga abinda yake kiwonta,

Daga Abdullahi Ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Dukkaninku masu kiwone to abin tambayane daga abinda yake kiwonta, shugaban mutane mai kiwo ne shi abin tambayane game da su, mutum mai kiwone ga iyalan gidansa kuma shi abin tambaya ne game da su, mace mai kiwo ce a dakin mijinta da ’yayansa kuma ita abar tambaya ce game da su,, bawa mai kiwo ne akan dukiyar shugabansa shi abin tambaya ne game da ita, ku saurara dukkaninku abin tambaya ne game da abin da aka ba shi kiwonsa".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa akwai nauyi akan kowanne musulmi a cikin zamantakewa da zai kula da ita kuma take akan sa, Shugaba da sarki mai kiwo ne a abinda Allah Ya ba shi kulawarsa, to ya wajaba akansa kiyaye shari'unsu, da kiyayesu daga wanda zai zalincesu, da yakar makiyinsu, da rashin tozarta hakkokinsu, Mutum a iyalan gidansa wanda aka dorawa tsayuwa kula da su ne da ciyar da su, da kyakkyawar mu'amala, da koyar da su da ladabtar da su, mace a cikin gidan mijinta mai kiwo ce ta hanyar kyawun sarrafa gidansa, da tarbiyyar 'ya'yansa, kuma ita abar tambaya ce game da hakan, bawa wanda aka mallaka da wanda aka yake aiki a biya shi abin tambaya ne a dukiyar mai gidansa ta hanyar tsayuwa da kiyaye abinda ke hannunsa daga gare shi , da hidimarsa, kuma shi abin tambaya ne game da hakan, kowanne mutum mai kiwo ne a abinda aka ba shi kiwon sa, kuma kowa abin tambaya ne game da abin kiwonsa.

فوائد الحديث

Nauyi a cikin al’umma ta Musulmai gamamman al’amari ne, kuma kowa da gwargadansa da ikonsa da kuma nauyin da aka dora masa.

Girman nauyin da yake kan mace, hakan ta hanyar tsayuwa da hakkin gidan mijinta da wajibin dake kanta na 'ya'yanta.

التصنيفات

Abubuwan da suka Wajaba kan Shugaba, kyawawan Halayya tsakanin Ma'aurata, Tarbiyyara Yara