Ku dinga maimaita wannan Alƙur’anin, ina rantse muku da wanda ran Muhammad yake a hannunSa ya fi saurin kufcewa sama da raƙumin da ya ke a dabaibayi

Ku dinga maimaita wannan Alƙur’anin, ina rantse muku da wanda ran Muhammad yake a hannunSa ya fi saurin kufcewa sama da raƙumin da ya ke a dabaibayi

Daga Abu Musa Al-ash'ariy Allah Ya yarda da shi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Ku dinga maimaita wannan Alƙur’anin, ina rantse muku da wanda ran Muhammad yake a hannunSa ya fi saurin kufcewa sama da raƙumin da ya ke a dabaibayi.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi umarnin yawan maimaita Alƙur’ani da dagewa a kan karanta shi; domin kada a manta bayan an haddace shi a zuciya, [Annabi] tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kuma ƙarfafi hakan da rantsuwa a kan Alƙur’ani ya fi saurin ɓacewa da tafiya daga zuciya a kan raƙumi da aka ɗaure, ga shi a ɗaure da igiya a ƙwauri, idan mutum yana yawan bibiyarsa sai ya riƙeshi, idan kuma ya sakeshi sai ya tafi ya ɓace.

فوائد الحديث

Idan mahaddacin Alƙur’ani ya dage lokaci bayan Lokaci zai kasance yana nan a haddace a zuciyarsa, idan kuwa ba haka ba sai ya tafi ya manta da shi.

Daga cikin fa'idojin bibiyar Alkur’ani akwai: samun lada, da ɗaukakar daraja a ranar Alkiyama.

التصنيفات

Falalar Kulawa da Al-qur’ani