إعدادات العرض
Wanda ya kyautata a Musulunci ba za'a kama shi da abinda ya aikata ba a lokacin Jahiliyya, wanda kuma ya munana a cikin Musulunci za'a kama shi da na farko da na karshe
Wanda ya kyautata a Musulunci ba za'a kama shi da abinda ya aikata ba a lokacin Jahiliyya, wanda kuma ya munana a cikin Musulunci za'a kama shi da na farko da na karshe
Daga Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi- ya ce: Wani mutum ya ce: ya Manzon Allah, shin za'a kamamu da abinda muka aikata a lokacin Jahiliyya? ya ce: "Wanda ya kyautata a Musulunci ba za'a kama shi da abinda ya aikata ba a lokacin Jahiliyya, wanda kuma ya munana a cikin Musulunci za'a kama shi da na farko da na karshe".
الترجمة
العربية Kurdî English Kiswahili Español اردو Português বাংলা Bahasa Indonesia فارسی தமிழ் हिन्दी සිංහල Tiếng Việt മലയാളം Русский မြန်မာ ไทย پښتو অসমীয়া Shqip Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá Nederlands ئۇيغۇرچە Türkçe Bosanski తెలుగు دری Ελληνικά Azərbaycan Български Fulfulde Italiano ಕನ್ನಡ Кыргызча Lietuvių Malagasy or Română Kinyarwanda Српски тоҷикӣ O‘zbek नेपाली Moore Oromoo Wolof Tagalog Soomaali Français Українська bm Deutsch ქართული Македонски Magyar 中文الشرح
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana falalar shiga Musulunci. Kuma cewa wanda ya musulunta kuma ya kyautata Musuluncinsa ya zama mai tsarkakewa mai gaskiya, to ba za’a yi masa hisabi da abinda ya aikata na sabo ba a lokacin Jahiliyya, Wanda ya munana a cikin Musulunci, da ya zama munafiki ko ya yi ridda ga Addininsa, za'a yi masa hisabi da abinda ya aikata a cikin kafirci, da kuma abinda ya aikata a cikin Musulunci.فوائد الحديث
Himmatuwar sahabbai - Allah Ya yarda da su - da kuma tsoronsu daga abinda ke tare da su na ayyukan Jahiliyya (da suka yi a baya).
Kwadaitarwa akan tabbata akan Musulunci.
Falalar shiga addinin Musulunci, kuma cewa shi yana kankare ayyukan da suka gabata.
Wanda ya yi ridda da munafiki za’a yi masa hisabi da dukkanin wani aikin da ya gabatar a lokacin Jahiliyya, haka ma kuma da dukkanin wani zinibin da ya aikata shi a cikin Musulunci.