إعدادات العرض
Idan Ramadan ya zo to ki yi umara, domin umara a cikinsa yana daidai da Hajji
Idan Ramadan ya zo to ki yi umara, domin umara a cikinsa yana daidai da Hajji
Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce wa wata mata daga mutanen Madina, Ibnu Abbas ya ambaceta sai na manta sunanta: "Meya hanaki ki yi Hajji tare da mu?" Ta ce: Ba mu da komai sai raƙuma biyu, sai baban ɗanta da ɗanta suka yi Hajji akan raƙumi ɗaya, kuma ya bar mana ɗayan muna ban ruwa da shi, ya ce: "Idan Ramadan ya zo to ki yi umara, domin umara a cikinsa yana daidai da Hajji".
[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Tiếng Việt ئۇيغۇرچە Kurdî മലയാളം Kiswahili Português සිංහල دری Svenska አማርኛ অসমীয়া ไทย Yorùbá Кыргызча ગુજરાતી Malagasy नेपाली Oromoo Română Nederlands Soomaali پښتو తెలుగు Kinyarwanda ಕನ್ನಡ Српски Wolof Moore Lietuvių ქართული Українськаالشرح
Lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya dawo daga Hajjin ban kwana, sai ya cewa wata mata daga mutanen Madina wacce bata yi Hajji ba: Me yahanaki yin Hajji tare da mu? Sai ta kawo hanzarin cewa suna da raƙuma biyu ne, sai mijinta da ɗanta suka yi Hajji akan ɗayan su, kuma ya bar ɗayan dan su yi ban ruwa da shi daga rijiya. Sai Annabi - tsira da aminci su tabbata agare shi - ya bata labarin cewa yin Umura a watan Ramadan ladansa ya yi daidai da ladan Hajji.فوائد الحديث
Falalar Umra a cikin watan Ramadan.
Umra a Ramadan tana daidai da Hajji a lada, ba a sarayar da Hajjin farilla ba.
Ladan ayyuka yana ƙaruwa da ƙaruwar ɗaukakan lokuta, daga hakan akwai ayyuka a cikin Ramadan.
التصنيفات
Falalar Hajji da Umra