إعدادات العرض
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi layya da raguna biyu masu farar fuska da baƙi-baƙi masu ƙaho, ya yanka su da hannunsa, kuma ya ambaci Allah ya yi kabbara, ya ɗora ƙafarsa akan fatun wuyayensu
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi layya da raguna biyu masu farar fuska da baƙi-baƙi masu ƙaho, ya yanka su da hannunsa, kuma ya ambaci Allah ya yi kabbara, ya ɗora ƙafarsa akan fatun wuyayensu
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi layya da raguna biyu masu farar fuska da baƙi-baƙi masu ƙaho, ya yanka su da hannunsa, kuma ya ambaci Allah ya yi kabbara, ya ɗora ƙafarsa akan fatun wuyayensu.
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी ئۇيغۇرچە Português മലയാളം Kurdî অসমীয়া Kiswahili አማርኛ Tiếng Việt ગુજરાતી Nederlands සිංහල پښتو ไทย नेपाली Кыргызча Malagasy Svenska Română తెలుగు ქართულიالشرح
Anas - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yanka raguna biyu wato mazan tumakai, masu fararen ƙahunhuna waɗanda baƙi ya cakuɗa da su, kuma ya ce: Da sunan Allah, Allah ne Mafi girma, kuma ya ɗora ƙafarsa akan wuyansu.فوائد الحديث
Halaccin layya, haƙiƙa musulmai sun haɗu akanta.
Abin da ya fi layya ta zama daga wannan nau'in da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi layya da shi; dan kyan ganinsa da kuma kasancewar kitsensa da namansa yafi daɗi.
AlNawawi ya ce: A cikinsa cewa an so mutum ya jiɓinci yanka layyarsa da kansa, kada ya wakilta a yankata sai da wani uzuri, a wannan lokacin an so ya halacci yankanta, idan ya wakilta wani musulmi ya halatta babu wani saɓani.
Ibnu Hajar ya ce: A cikinsa akwai son kabbara tare da basmala a lokacin yanka da son ɗora ƙafar dama akan fatar wuyan abin layyar, kuma sun haɗu akan cewa kwantar da ita yana kasancewa ne a ɓangaren hagu sai ya ɗora ƙafaresa akan ɓangaren dama dan ya zama ya fi sauƙi ga mai yankan a wurin riƙe wuƙa da dama, da riƙe kanta da hannunsa na hagu.
An so layya da mai ƙaho kuma yana halatta da waninsa.