Kada ɗayanku ya kuskura ya taɓa azzakarinsa da damansa, a halin yana fitsari, kuma kada ya yi tsarki na bayan gida da damansa, ko kuma ya yi nunfashi a ƙwarya

Kada ɗayanku ya kuskura ya taɓa azzakarinsa da damansa, a halin yana fitsari, kuma kada ya yi tsarki na bayan gida da damansa, ko kuma ya yi nunfashi a ƙwarya

Daga Abu Katada - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ɗayanku ya kuskura ya taɓa azzakarinsa da damansa, a halin yana fitsari, kuma kada ya yi tsarki na bayan gida da damansa, ko kuma ya yi nunfashi a ƙwarya".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana wasu ladubba; yayin da ya hana mutum ya riƙe azzakarinsa a halin fitsari da hannunsa na dama, ko kuma a gusar da najasa daga gaba ko baya da hannun dama; domin dama an tanadeta ne dan manyan abubuwa, kamar yadda ya yi hani mutum ya yi numfashi a cikin ƙwaryar (kofi) da yake sha acikinta.

فوائد الحديث

Bayanin rigayar musulunci a ladubba da tsafta.

Nisantar abubuwan ƙazanta, idan an yi buƙatuwa zuwa taɓa su, to ya kasance da hagu ne.

Bayanin matsayin dama da falalarta akan hagu.

Cikar shari'ar musulunci da tarowar koyarwarta.

التصنيفات

Ladaban cin Abinci da Shan Abun Sha, Ladaban biyan bukata