Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance mafi tsananin kunya daga budurwar dake cikin budircinta, idan ya ga wani abinda yake kinsa muna gane hakan a fuskarsa

Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance mafi tsananin kunya daga budurwar dake cikin budircinta, idan ya ga wani abinda yake kinsa muna gane hakan a fuskarsa

Daga Abu Sa'id al-Kudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance mafi tsananin kunya daga budurwar dake cikin budircinta, idan ya ga wani abinda yake kinsa muna gane hakan a fuskarsa.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Abu Sa'idul Khudr - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance mafi tsananin kunya daga yarinya budurwa wacce bata yi aure ba, ba ta yi mu'amala da maza ba wacce ke suturce a cikin gidanta, yana daga tsananin kunyarsa cewa shi idan ya ki wani abu fuskarsa tana canjawa kuma ba ya magana, kai sahabbansa suna fahimtar kinsa ga hakan a fuskarsa.

فوائد الحديث

Bayanin abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kunsa akansa na kunya, ita ce ɗabi'u masu girma.

Kunyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - muddin dai ba'a keta alfarmomin Allah, idan an keta su; to shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana fushi yana umartar sahabbansa kuma yana hanasu.

Kwaɗaitarwa akan ɗabi'antuwa da kunya; domin ita tana sawa rai aiki mai kyau da barin mummuna.

التصنيفات

Kunyarsa SAW