Mafi kusancin lokacin da bawa yake kasancewa kusa da Ubangiji a cikin (kason) dare na karshe

Mafi kusancin lokacin da bawa yake kasancewa kusa da Ubangiji a cikin (kason) dare na karshe

Daga Abu Umamah ya ce: Amr ɗan Abasa - Allah Ya yarda da shi - ya zantar da ni cewa shi ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Mafi kusancin lokacin da bawa yake kasancewa kusa da Ubangiji a cikin (kason) dare na karshe, idan kana da ikon ka kasance daga wanda yake ambatan Allah a wannan lokacin to ka kasance".

[Ingantacce ne]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa Ubangiji - tsarki ya tabbatar maSa - Shi ne mafi kusa ga bawa a lokacin sulusin dare na karshe; idan an datar da kai kuma ka samu iko - ya kai mumini - da ka kasance daga jumlar masu bauta masu sallah masu ambatan Allah masu tuba a wannan lokacin to shi wani al'amari ne wanda yana kamata a ci ribarsa da kokari a cikinsa.

فوائد الحديث

Kwaɗaitar da musulmi akan zikiri a karshen dare.

Fifikon lokuta a tsakaninsu ga zikiri da addu'a da sallah.

Mirik ya ce: A cikin banbanci tsakaknin faɗinsa: "Mafi kusancin lokacin da Ubangiji ya fi kusa da bawa", da tsakanin faɗinsa: " Mafi kusancin lokacin da bawa yake kusa da Ubangijinsa alhali shi yana mai sujjada': Abin nufi a nan bayanin lokacin kasancewar Ubangiji Shi ne mafi kusa ga bawa shi ne tsakiyar dare, abin nufi a can bayanin kusancin halayen bawa ga Ubangiji alhali shi yana halin sujjada.

التصنيفات

Sababan Amsa Addu’a da kuma abubuwan da suke hana su