Kowacce gaɓa daga (jikin) mutane akwai sadaka a kanta

Kowacce gaɓa daga (jikin) mutane akwai sadaka a kanta

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kowacce gaɓa daga (jikin) mutane akwai sadaka a kanta, kowanne yinin da rana ta fito a cikin sa da (mutum) zai daidaita tsakanin mutune biyu sadaka ne, kuma ya taimaki mutum game da dabbar sa; sai ya ɗora shi a kanta, ko ya ɗauke masa kayan sa a kanta, to, sadaka ne, kuma kalma mai daɗi sadaka ce, kuma kowanne taku da zai yi zuwa sallah sadaka ne, kuma ya kau da ƙazanta daga hanya sadaka ne".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa akwai sadaka ta ɗawwu'i saboda Allah - Maɗaukakin sarki - akan kowanne musulmi mukallafi a kowacce rana a kan kowacce gaba daga cikin gabban jikinsa, sadaka ta Nafila ga Allah madaukakin sarki akan tafarkin godiya gare Shi akan lafiya, kuma sanya ƙasusuwansa gaɓɓai zai samu dama da suna damƙa da shinfiɗawa. kuma cewa wannan sadakar tana kaiwa ga ayyukan alheri gabaɗayanta bata tsayuwa akan bada wata dukiya, Daga ciki: Daidaitawarka da yin sulhunka tsakanin masu husuma sadaka ne. A taimakonka ga wani gajiyayye a dabbarsa (abin hawa) sai ka ɗora shi akanta, ko ka ɗauke masa kayansa sadaka ne. Kalma mai daɗi ta zikiri ce da addu'a da sallama da wasunsu sadaka ce. Kowanne takin da ka yi tafiya da shi zuwa sallah sadaka ne, kawar da abinda ake cutuwa da shi a hanya sadaka ne.

فوائد الحديث

Tsarin ƙasusuwan ɗan Adam da lafiyarsu yana daga mafi girman ni'imomin Allah - Maɗaukakin sarki - akan mutum, to kowanne ƙashi daga cikinsu yana buƙatuwa zuwa ga sadaka daga gare shi a karankansa dan godiyar wancan ni'imar ta cika.

Kwaɗaitarwa akan jaddada godiya a kowacce rana dan dawwaamar da waɗancan ni'imomin.

Kwaɗaitarwa a kan dawwama da nafilifili da sadakoki Kowacce rana.

Falalar yin sulhu tsakanin mutane.

Zaburarwa akan taimakon mutum ga ɗan'uwansa; domin taimakonsa gare shi sadaka ne.

Zaburarwa akan halartar sallar jam'i da tafiya zuwa gareta, da raya masallatai da hakan.

Wajabcin girmama hanyoyin musulmai ta hanyar nisantar da abinda zai kware su ko ya cutar da su.

التصنيفات

Falalar musulunci da kyawawan koyarwarsa