إعدادات العرض
Lallai shi bai taba fada ba koda yini daya: Ya Ubangiji Ka gafarta mini kuskurena ranar sakamako
Lallai shi bai taba fada ba koda yini daya: Ya Ubangiji Ka gafarta mini kuskurena ranar sakamako
Daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na ce: Ya Manzon Allah, Ibn Jud'an ya kasance a lokacin jahiliyya yana sada zumunci, yana ciyar da miskinai, shin hakan zai anfanar da shi? Sai Ya ce: "Ba zai anfanar dashi ba, Lallai shi bai taba fada ba koda yini daya: Ya Ubangiji Ka gafarta mini kuskurena ranar sakamako".
[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]
الترجمة
العربية English မြန်မာ Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá Nederlands اردو Español Bahasa Indonesia ئۇيغۇرچە বাংলা Türkçe Bosanski සිංහල हिन्दी Tiếng Việt Kurdî മലയാളം తెలుగు Kiswahili ไทย پښتو অসমীয়া Shqip دری Ελληνικά Български Fulfulde Italiano ಕನ್ನಡ Кыргызча Lietuvių Malagasy or Română Kinyarwanda Српски тоҷикӣ O‘zbek नेपाली Moore Oromoo Wolof Soomaali Tagalog Français Azərbaycan Українська bm தமிழ் Deutsch ქართული Português Македонски Magyar فارسی Русский 中文الشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari game da Abdullahi Ibnu Jud'an, ya kasance yana daga shugabannin Kuraishawa kafin Musulunci, Yana daga kyawawan ayyukansa cewa shi: Yana sada zumuncin 'yan uawansa, yana ciyar da miskinai, da wasunsu daga cikin mafifitan ayyukan da Musulunci ya kwadaitar akan aikatasu, da cewa wadannan ayyukan ba za su anfanar da shi a lahirarsa ba; saboda kafircewarsa ga Allah, kuma shi bai taba fada ba ko sau daya: Ya Ubangiji ka gafarta mini kuskurena ranar sakamako.فوائد الحديث
Bayanin falalar imani, kuma shi (imani) sharadine na karbar ayyuka.
Bayanin shu'umancin kafirci, kuma shi (kafirci) yana daga masu bata ayyuka na gari.
Kafirai ayyukansu ba za su anfanar da su a lahira ba, saboda rashin imaninsu da Allah da kuma ranar lahira.
Ayyukan mutum acikin halin kafircinsa za'a rubuta masa su idan ya musulunta, kuma za’a yi masa sakayya akansu.