Kada ku riƙi gona sai ku yi kwaɗayin duniya

Kada ku riƙi gona sai ku yi kwaɗayin duniya

Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kada ku riƙi gona sai ku yi kwaɗayin duniya".

[Hasan ne ta wani Sanadin]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani daga riƙon gona; domin hakan yana daga sabubban kwaɗayi a duniya da karkata zuwa gareta abar lahira.

فوائد الحديث

Hani akan yawaita neman duniya da abinda yake kaiwa zuwa juyawa lahira baya.

A cikin hadisin babu hani daga riƙon binda yake akwai abin samun rayuwa daga gare shi, kaɗai hani ne daga dulmiya a cikin duniya da kuma mantawa da lahira.

Sindi ya ce: Abin nufi: Kada ku zirfafa a cikin riƙon gona sai ku shagalta da ita daga ambatan Allah.

التصنيفات

Falaloli da Ladabai, Zargin Son Duniya