Ya manzon Allah, muna ganin yaƙi shi ne mafificin aiki, shin ba ma yi yaƙi ba? ya ce: "A'a, sai dai mafificin yaƙi: Shi ne kubutaccen aikin Hajji

Ya manzon Allah, muna ganin yaƙi shi ne mafificin aiki, shin ba ma yi yaƙi ba? ya ce: "A'a, sai dai mafificin yaƙi: Shi ne kubutaccen aikin Hajji

Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Ya manzon Allah, muna ganin yaƙi shi ne mafificin aiki, shin ba ma yi yaƙi ba? ya ce: "A'a, sai dai mafificin yaƙi: Shi ne kubutaccen aikin Hajji".

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]

الشرح

Sahabbai - Allah Ya yarda da su - sun kasance suna ganin yaƙi a tafarkin Allah da yakar maƙiya yana daga mafifitan ayyuka, sai Nana A'isah - Allah Ya yarda da ita - ta tambayi annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa zasu iya yin yaƙi? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya nuna musu mafificin yaƙi a cikin haƙƙinsu shi ne kubutaccen aikin Hajji wanda ya dace da AlKur'ani da Sunnah, wanda ya kubuta daga zunubi da kuma riya.

فوائد الحديث

Yaƙi yana daga mafifitan ayyuka ga maza.

Hajji ga mata ya fi jihadi, kuma shi yana daga mafifitan ayyuka a gare su.

Ayyuka suna fifitar juna gwargwadan mai aikin.

An ambaci Hajji Jihadi; domin cewa shi jihadi ne na rai, kuma a cikinsa akwai bada dukiya, da ƙarfin jiki, shi ibada ce ta jiki da dukiya kamar yaƙi a tafarkin Allah.

التصنيفات

Falalar Hajji da Umra