Wanda ya yi kira zuwa ga shiriya yana da lada kwatankwacin ladaddakin wadanda suka bi shi, ba za’a tauye komai daga ladansu ba

Wanda ya yi kira zuwa ga shiriya yana da lada kwatankwacin ladaddakin wadanda suka bi shi, ba za’a tauye komai daga ladansu ba

Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Wanda ya yi kira zuwa ga shiriya yana da lada kwatankwacin ladaddakin wadanda suka bi shi, ba za’a tauye komai daga ladansu ba, wanda ya yi kira zuwa ga bata yana da zunubi kwatankwacin zunuban wadanda suka bi shi, ba za’a tauye komai daga zunubansu ba".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa wanda ya shiryar ya kwadaitar da mutane kan hanyar da aciknta akwai gaskiya da alheri da fada ne ko aikatawa yana da ladan wanda ya bi shi ba tare da antauye komai daga ladan mai bin ba. Wanda ya kira mutane zuwa hanyar karya da sharri a cikinta akwai zunubi da kuskure ko wani al'amarin da ba ya halatta, na fadane ko aikatawa, ya kasance akwai zunubi akansa kwatankwacin zunubin wanda ya bi shi ba tare da an tauye komai daga zunubansu ba.

فوائد الحديث

Falalar kira zuwa shiriya, kadan ce ko da yawa, kuma cewa mai kira yana da ladan mai aikin, hakan yana daga girman falalar Allah da cikar karamcinSa.

Hadarin kira zuwa ga bata kadan ce ko da yawa, kuma mai kiran yana da zununubi kwatankwacin zunubin wanda ya aikata.

Sakamako yana daga jinsin aiki, wanda ya yi kira zuwa alheri yana da ladan wanda ya aikata shi, wanda ya yi kira zuwa ga sharri yana da zunubi kwatankwacin zunubin wanda ya aikata shi.

Ya wajaba akan musulmi ya kiyayi a yi koyi da shi dan bayyanar da sabonsa ga mutane suna kallonsa, cewa shi zai yi laifi da wanda ya kwaikwayeshi koda bai zaburar da shi akan hakan ba.

التصنيفات

Bidi'a