Yaku mutane na haneku da wuce gona da iri a addini, kadai wuce gona da iri a addini shi ya halaka wadanda ke gabanku

Yaku mutane na haneku da wuce gona da iri a addini, kadai wuce gona da iri a addini shi ya halaka wadanda ke gabanku

Daga Abdullahi Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce a washegarin jifan babban shaidan alhali shi yana kan taguwarsa: "Ka tsintomin tsakwankwani". sai na tsinto masa tsakwankwani bakwai, su tsakwankwani ne na harbi, sai ya fara yana motsasu a tafinsa yana cewa: "Misalan wadananan sai ku yi jifa (da su)”. sannan ya ce: "Yaku mutane na haneku da wuce gona da iri a addini, kadai wuce gona da iri a addini shi ya halaka wadanda ke gabanku".

[Ingantacce ne]

الشرح

Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - yana bada labarin cewa shi ya kasance tare da Annabi - tsira da amincin Alah su tabbata agare shi - a ranar babbar sallah wayewar garin jifan babban Shaidan a hajjin bankwana, sai ya umarce shi ya tsinto masa tsakwankwanin jifa, sai ya tsinto masa tsakwankwani bakwai, kowacce daya daga cikinsu ta kai girman wake ko bunduq, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -ya sanya su a hannu sa, sannan ya motsa su, ya ce: Ku yi jifa da kwatankwacin wannan a girma, sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargadar daga wuce gona da iri da tsanantawa da ketare iyaka a al'amuran addini, kadai ketare iyaka da wuce gona da iri da tsanantawa a addini shi ya halaka al'ammomin da suka gabata.

فوائد الحديث

Hani daga wuce gona da iri a addini, da bayanin mummunan karshensa, kuma shi ne sababi na halaka.

Izina da wadanda suka rigayemu daga al'ummu dan nisantar abinda suka afka cikinsa na kuskure.

Kwadaitarwa akan koyi da sunna.

التصنيفات

Mas’alolin Jahiliyya