إعدادات العرض
1- cewa an tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - game da ambulaf? Ya ce: Aikin Iblis ne.
2- Baya tare da mu Duk wanda yai canfi ko aka yi masa, ko yayi Bokanci ko aka yi masa ko yayi Sihiri ko aka yi masa; kuma duk wanda ya je wajen Boka kuma ya gasgata shi cikin abinda ya ke fada; to hakika ya kafircewa abinda aka saukarwa Annabi.
3- Wannan kalmar ta gaske aljani ya fauceta ne, sai ya yi kyarkyararta a kunnen abokin harkarsa irin kyarkyarar kaza, sai su cakuɗata da ƙarya sama da ɗari
4- Yaku mutane na haneku da wuce gona da iri a addini, kadai wuce gona da iri a addini shi ya halaka wadanda ke gabanku
5- Babu adwa(harbin cututtuka ta kashin kansu) babu shu’umci babu camfi da mujiya, ba camfa watan safar
6- Wanda ya mari kunci ba shi daga cikinmu, ko ya yaga kuibin tufafi, ko yayi kira irin kiran jahiliyya