إعدادات العرض
Idan bawa yayi rashin lafiya ko yayi tafiya za'a rubuta masa tamkar abinda ya kasance yana aikatawa alhali yana zaman gida kuma lafiyayye
Idan bawa yayi rashin lafiya ko yayi tafiya za'a rubuta masa tamkar abinda ya kasance yana aikatawa alhali yana zaman gida kuma lafiyayye
Daga Abu Musa Al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan bawa yayi rashin lafiya ko yayi tafiya za'a rubuta masa tamkar abinda ya kasance yana aikatawa alhali yana zaman gida kuma lafiyayye".
[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Türkçe اردو 中文 हिन्दी Tagalog Kurdî Português മലയാളം తెలుగు Kiswahili தமிழ் සිංහල မြန်မာ Deutsch 日本語 پښتو Tiếng Việt অসমীয়া Shqip Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá Nederlands ئۇيغۇرچە ไทย دری Akan Български Fulfulde Magyar Italiano ಕನ್ನಡ Кыргызча Lietuvių Malagasy or Română Kinyarwanda тоҷикӣ O‘zbek नेपाली Moore Azərbaycan Wolof Oromoo Soomaali Українська bm km rn ქართული mk Српски lnالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bada labari game da falalar Allah da rahamarSa, kuma cewa musulmi idan ya kasance al'adarsa cewa yana aikata wani aiki na gari a halin lafiyarsa da kuma zaman gidansa, sannan wani uzuri ya faru da shi sai ya yi rashin lafiya bai samu damar yin sa ba, ko ya shagalta da tafiya bai samu ya yi shi ba, ko wani uzurin; to cewa shi za'a rubuta masa lada cikakke, kamar da ya aikata shi a halin lafiya da zaman gida.فوائد الحديث
Yalwal falalar Allah ga bayinSa.
Kwadaitarwa akan kokari a biyayya da cin ribar lokuta a halin lafiya da faraga.