Wanda ya yi tsayuwar dare a daren Lailatul ƙadari yana mai imani da neman lada za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa

Wanda ya yi tsayuwar dare a daren Lailatul ƙadari yana mai imani da neman lada za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya yi tsayuwar dare a daren Lailatul ƙadari yana mai imani da neman lada za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa"

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba da labari game da falalar tsayuwar Lailatul kadari wacce take kasancewa a goman ƙarshe na Ramadan, cewa wanda ya yi ƙoƙarin yin sallah a cikinta da addu'a da karatun al-ƙur'ani da zikiri, yana mai imani da ita, da kuma abin da ya zo a falalarta, yana mai kwaɗayin sakamakon Allah - Maɗaukakin sarki - da aikinsa, ba don riya ko jiyarwa ba, to, za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubansa.

فوائد الحديث

Falalar daren lailatul ƙadri da kwaɗaitarwa a kan tsayuwarsa.

Ayyuka na gari ba'a karɓarsu sai tare da gaskiyar niyyoyi.

Falalar Allah da rahamarsa, cewa wanda ya tsaya (da ibada) a daren Lailatul ƙadri yana mai imani da neman lada za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa.

التصنيفات

Tsayuwar Dare, Tsayuwar Dare, Goman Qarshe na Watan Azumi, Goman Qarshe na Watan Azumi