إعدادات العرض
Ya kai yaro, zan sanar da kai wasu kalmomi, ka kiyaye Allah Zai kiyayeka, ka kiyaye Allah zaka sameshi a daura da kai, idan za ka yi roƙo, to, ka roƙi Allah, idan za ka nemi taimako, to, ka nemi taimakon Allah
Ya kai yaro, zan sanar da kai wasu kalmomi, ka kiyaye Allah Zai kiyayeka, ka kiyaye Allah zaka sameshi a daura da kai, idan za ka yi roƙo, to, ka roƙi Allah, idan za ka nemi taimako, to, ka nemi taimakon Allah
Daga ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Na kasance a bayan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wata rana, sai ya ce: "Ya kai yaro, zan sanar da kai wasu kalmomi, ka kiyaye Allah Zai kiyayeka, ka kiyaye Allah zaka sameshi a daura da kai, idan za ka yi roƙo, to, ka roƙi Allah, idan za ka nemi taimako, to, ka nemi taimakon Allah, ka sani cewa da al'umma za su taru a kan su amfaneka da wani abu, ba za su amfaneka ba sai da abin da tabbas Allah Ya rubuta maka, da za su taru a kan su cutar da kai da wani abu, ba za su cutar da kai ba, sai da abin da tabbas Allah Ya rubuta a kanka, an ɗauke alƙaluma kuma takardu sun bushe".
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español Français Bahasa Indonesia Русский Türkçe اردو 中文 हिन्दी ئۇيغۇرچە Kurdî Português മലയാളം తెలుగు Kiswahili فارسی தமிழ் မြန်မာ Deutsch 日本語 پښتو Tiếng Việt অসমীয়া Shqip Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá Nederlands සිංහල ไทย دری Fulfulde Magyar Italiano ಕನ್ನಡ Кыргызча Lietuvių or Română Kinyarwanda Српски O‘zbek Moore नेपाली Malagasy тоҷикӣ Oromoo Wolof Soomaali Български Українська Azərbaycan Tagalog ქართული bm Македонски Ελληνικάالشرح
Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - yana ba da labarin cewa ya kasance yana ƙarami yana haye tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai (Annabi) tsira da aminci su tabbata a gare shi ya ce: Zan sanar da kai wasu al'amura da wasu abubuwan da Allah zai amfanar da kai su: Ka kiyaye Allah ta hanyar kiyaye umarninsa da nisantar hane-hanensa, ta inda Zai sameka a ayyukan biyayya da kusanci, ka da Ya sameka a ayyukan saɓo da zunubai, idan ka aikata haka sakamakonka zai kasance shi ne Allah Zai kiyayeka daga abubuwan ƙi na duniya da lahira, kuma Zai taimakeka a ayyukanka a duk inda ka fuskanta. Idan kayi nufin roƙon wani abu, to, kada ka roƙi kowa sai Allah, to, haƙiƙa Shi kaɗai ne wanda yake amsawa masu roƙo. Idan kayi nufin neman taimako, to, kada ka nemi taimakon kowa sai Allah. Kuma ya zama kana da yaƙini cewa wani amfani ba zai sameka ba, ko da mutanen duniya gaba ɗaya sun taru akan amfanarka sai dai abin da Allah Ya rubuta maka, kuma wani abin cutarwa ba zai faru a kanka ba, ko da mutanen duniya gaba ɗaya za su taru a kan cutarka, sai dai abin da Allah Ya ƙaddara a kanka. Kuma wannan al'amarin tabbas Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya rubuta maka ya kuma ƙaddara shi daidai da abin da hikimarsa da saninsa suka hukunta, babu canji ga abin da Allah Ya rubuta.فوائد الحديث
Muhimmancin sanar da yara al'amuran addini na tauhidi da ladubba da sauransu.
Sakamako yana kasancewa daga irin aikin da aka yi.
Umarni a kan dogaro ga Allah, da tawakkali gareshi ba da waninsa ba, madalla da Shi a matsayin wakili.
Imani da hukunci da ƙaddara da yarda da shi, kuma Allah Ya ƙaddara kowane abu.
Wanda ya tozarta umarnin Allah, to, Allah Zai tozartashi ba zai kiyayeshi ba.
التصنيفات
Matakan Hukuncin Allah da Qaddara