Mafi alherinku shi ne wanda ya koyi Alkur’ani kuma ya koyar da shi

Mafi alherinku shi ne wanda ya koyi Alkur’ani kuma ya koyar da shi

Daga Usman Allah Ya yarda da shi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi ya ce: "Mafi alherinku shi ne wanda ya koyi Alkur’ani kuma ya koyar da shi".

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da labarin mafi falalar Musulmai, wanda kuma yake ƙololuwar daraja a wurin Allah shi ne, wanda ya koyi Alƙur’ani, karatun da hadda da rerawa da fahimta da Tafsir. Ya kuma sanar da wani abin da yake wurinsa na iliman Alkur’ani (Ulumul Qur’an) tare da aiki da shi.

فوائد الحديث

Bayanin matsayin Alkur’ani, kuma shi ne mafificin zance; domin shi zancen Allah ne.

Mafificin masu koyo shi ne wanda yake sanar da waninsa, ba wai wanda ya taƙaitu a kansa kawai ba.

Koyon Alkur’ani da koyar da shi ya ƙunshi karatu da [sanin] ma’anoni da Hukunce Hukunce.

التصنيفات

Falalar Kulawa da Al-qur’ani