إعدادات العرض
Wanda ya je wurin Ɗan duba (malamin duba) ya tambaye shi wani abu, to, ba za a karɓi Sallarsa ta darare arba’in ba
Wanda ya je wurin Ɗan duba (malamin duba) ya tambaye shi wani abu, to, ba za a karɓi Sallarsa ta darare arba’in ba
Daga wasu cikin matan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: Wanda ya je wurin Ɗan duba (malamin duba) ya tambaye shi wani abu, to, ba za a karɓi Sallarsa ta darare arba’in ba.
الترجمة
العربية Bosanski English فارسی Français Bahasa Indonesia Русский اردو 中文 हिन्दी বাংলা Español Kurdî Português മലയാളം తెలుగు Kiswahili தமிழ் සිංහල မြန်မာ ไทย Deutsch 日本語 پښتو Tiếng Việt অসমীয়া Shqip Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá Nederlands ئۇيغۇرچە Türkçe دری Magyar Italiano ಕನ್ನಡ Кыргызча Lietuvių Malagasy Română Kinyarwanda नेपाली Српски Soomaali Moore Українська Български Tagalog Wolof Azərbaycanالشرح
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana tsoratarwa a kan zuwa wurin mai duba -suna ne fitacce na boka, da mai taurari, mai zane a kasa da makamantansu, irin wanda yake kafa dalilin sanin gaibu ta hanyar wasu abubuwa na farko-farkon lamari- zallar tambayarsa a kan wani abu na gaibu, zai haramta masa ladan sallah na kwanaki arba’in, wannan uƙuba ce, a kan wannan laifi, kuma zunubi ne mai girma.فوائد الحديث
Haramcin bokanci, da zuwa wurin boka da kuma tambayarsu gaibu.
Tabbas ana hanawa mutum ladan biyayya don ya zama uƙuba a gare shi a kan aikata laifi.
Yana shiga cikin wannan Hadisin abin ake cewa burji da duba shi, da karanta tafin hannu, da ƙwarya, ko da kuwa leƙawa ne kaɗai, domin duka yana cikin bokanci, kuma yana cikin iƙirarin sanin gaibu.
Idan wannan ya zama sakamakon wanda ya je wurin mai duba, to, ya ya halin shi mai duban.??
Sallar kwanaki arba’in idan ya yi ba ta yi ba, kuma ba zai rama ta ba, saidai babu ladanta.
التصنيفات
Sunaye da Hukunce Hukunce