Dukkan wanda ya ɗosani wani yanki na ilimin taurari, to, haƙiƙa ya ɗosani wani yanki na tsafi, ya ƙara abin da ya ƙara

Dukkan wanda ya ɗosani wani yanki na ilimin taurari, to, haƙiƙa ya ɗosani wani yanki na tsafi, ya ƙara abin da ya ƙara

Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Dukkan wanda ya ɗosani wani yanki na ilimin taurari, to, haƙiƙa ya ɗosani wani yanki na tsafi, ya ƙara abin da ya ƙara".

[Ingantacce ne]

الشرح

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayyana duk wanda ya koyi, ya samu wani tsagi na ilimin taurari da buruji da kuma kafa dalili da motsinsu da shigarsu da fitarsu a kan abin da zai faru a bayan ƙasa na mutuwar wane, ko rayuwarsa, ko rashin lafiyarsa, da makamancin haka cikin abinda zai faru nan gaba, to, haƙiƙa ya koyi wani tsagi na sihiri, kuma duk lokacin da mutum ya ƙara wannan ilimin, to, ya ƙara asiri [tsafi] ne.

فوائد الحديث

Haramcin ilimin taurari wanda yake na ba da labarin abin da zai faru nan gaba, dogaro da yanayin taurari, domin yana cikin iƙirarin sanin gaibu.

Ilimin taurari haramun ne, yana cikin nau’ukan asiri [tsafi] wanda yake kore Tauhidi, saɓanin nazarin taurari domin sanin inda mutum ya nufa, ko sanin alƙibla, ko sanin shigar lokacin wasu bukukuwa, ko watanni, to, wannan ya halatta.

Duk lokacin da ya ƙara a koyar ilimin taurari, to, yana ƙara koyar wani kaso ne na asiri [tsafi].

Taurari suna da fa'idoji uku, Allah ya ambace su a LittafinSa: Ƙawa ga sama, alamomi da za’a dinga ganewa da su, jifa ga shaiɗanu.

التصنيفات

Abubuwan da suke warware