إعدادات العرض
Wanda ya ga wani mummunan abu daga cikinku, to ya canza shi da hannunsa, idan ba zai iya ba to (ya canza shi) da harshe, idan ba zai iya ba to (ya canza shi) da zuciyarsa, wannan shi ne mafi raunin imani
Wanda ya ga wani mummunan abu daga cikinku, to ya canza shi da hannunsa, idan ba zai iya ba to (ya canza shi) da harshe, idan ba zai iya ba to (ya canza shi) da zuciyarsa, wannan shi ne mafi raunin imani
Daga Abu Sa'id Al-Kudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- yana cewa: "Wanda ya ga wani mummunan abu daga cikinku, to ya canza shi da hannunsa, idan ba zai iya ba to (ya canza shi) da harshe, idan ba zai iya ba to (ya canza shi) da zuciyarsa, wannan shi ne mafi raunin imani".
الترجمة
العربية Kurdî English Kiswahili Español اردو Português বাংলা Bahasa Indonesia فارسی தமிழ் हिन्दी සිංහල Tiếng Việt മലയാളം Русский မြန်မာ ไทย پښتو অসমীয়া Shqip Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá Nederlands ئۇيغۇرچە Türkçe Bosanski తెలుగు دری Ελληνικά Azərbaycan Български Fulfulde Italiano ಕನ್ನಡ Кыргызча Lietuvių Malagasy or Română Kinyarwanda Српски тоҷикӣ O‘zbek नेपाली Moore Oromoo Wolof Tagalog Soomaali Français Українська bm Deutsch ქართული Македонски Magyar Lingala 中文الشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana yin umarni da canza abin ki - shi ne dukkanin abinda Allah da ManzonSa suka hana - gwargwadon iko, Idan ya ga wani abin ki to yana wajaba akansa ya canja shi da hannu idan yana da iko, Idan ya gajiya ga hakan, to ya canja shi da harshensa, ta hanyar hana mai aikatawar, kuma ya bayyana masa cutar hakan, ya kuma shiryar da shi zuwa alheri maimakon wannan sharrin, Idan ya gajiya daga wannan matakin, to ya canja shi da zuciyarsa shi ne ya ki wannan mummunan aikin, kuma ya yi niyyar cewa shi da yana da iko akan canja shi to da ya aikata, canjawa da zuciya shi ne mafi raunin matakan imani a canja abin ki.فوائد الحديث
Hadisn asali ne a bayanin matakan canja abin ki.
Umarni da bi sannu-sannu a hani ga abin ki, kowa gwargwadon iyawarsa da ikonsa.
Hani daga abin ki wani babi ne mai girma a Addini kuma ba ya saraya akan wani mutum, kuma ana dorawa kowanne musulmi shi gwargwadon ikonsa.
Umarni da aikin alheri da hani daga abin ki yana daga dabi'un imani, kuma imani yana karuwa yana kuma raguwa.
Ana sharadantawa a hani daga abin ki: Sanin cewa wannan aikin abin ki ne.
Ana sharadantawa a canja abin ki: Cewa kada wani abin kin mafi girma daga gare shi ya biyo baya.
Akwai wasu ladubba da sharuddan da yake kamata ga musulmi ya sansu ga hani daga abin ki.
Hani daga abin ki yana bukatuwa zuwa ga siyasa ta shari'a, kuma da ilimi da basira.
Rashin inkari da zuciya yana nuni ga raunin imani.