Shin dayanku yana son idan ya koma zuwa iyalansa ya samu manyan taguwowi masu ciki masu giba?

Shin dayanku yana son idan ya koma zuwa iyalansa ya samu manyan taguwowi masu ciki masu giba?

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shin dayanku yana son idan ya koma zuwa iyalansa ya samu manyan taguwowi masu ciki masu giba?" muka ce: Eh. Ya ce; "To ayoyi uku dayanku zai karantasu a cikin sallarsa sun fiye masa alheri daga taguwowi uku manya masu ciki".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa ladan karanta ayoyi uku a cikin sallah; shi ne mafi alheri daga mutum ya sami taguwowi uku masu ciki manya a cikin gidansa.

فوائد الحديث

Bayanin falalar karanta Alkur’ani a cikin sallah.

Ayyuka na gari su ne mafi alheri kuma mafi wanzuwa daga jin dadin duniya mai karewa.

Wannan falalar ba ababen kayyadewa bane da karanta ayoyi uku kawai; duk lokacin da mai sallah ya kara karanta ayoyi a cikin sallarsa ladanta zai zama mafi alheri gare shi daga adadinsu daga taguwowi masu ciki.

التصنيفات

Falalar al-qur'ani Maigirma