Mala'iku ba sa tafiya da ayarin da a cikinsa akwai kare ko ƙararrawa

Mala'iku ba sa tafiya da ayarin da a cikinsa akwai kare ko ƙararrawa

Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Mala'iku ba sa tafiya da ayarin da a cikinsa akwai kare ko ƙararrawa".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Mala'iku ba sa tafiya a ayari a atare dasu akwai kare, ko ƙararraar da ake ratayawa a wuyan dabbobi, sai ya fara kara idan an dabbar na tafiya.

فوائد الحديث

Hani daga daukar karnuka da tafiya da su, in banda karen farauta ko na gadi.

Mala'iku wadanda ba sa tafiya da (karnuka da kararrawa) su ne Mala'ikun rahama, amma masu rubuta ayyukan bayi to su ba sa rabuwa da bayi a zamansu da tafiye-tafiyensu.

Hani daga ƙararrawa; Domin cewa ita garayace daga garayoyin shaidan, kuma a cikinta akwai kamanceceniya da gangar kiristoci.

Ya wajaba akan musulmi ya yi kwadayi akan nisanta da dukkanin abinda sha'aninsa shi ne nisantar da mala'iku daga gare shi.

التصنيفات

Mala’iku