An tambayi manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da mutumin da yake yaƙi dan jarumta, (da wanda) yake yaƙi dan ƙabilanci, (da wanda) yake yaƙi dan riya, wanne ne saboda Allah? sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: @"Wanda ya yi yaƙi…

An tambayi manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da mutumin da yake yaƙi dan jarumta, (da wanda) yake yaƙi dan ƙabilanci, (da wanda) yake yaƙi dan riya, wanne ne saboda Allah? sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: @"Wanda ya yi yaƙi dan kalmar Allah ta zama maɗaukakiya, to shi ne sabo da Allah".

Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: An tambayi manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da mutumin da yake yaƙi dan jarumta, (da wanda) yake yaƙi dan ƙabilanci, (da wanda) yake yaƙi dan riya, wanne ne saboda Allah? sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya yi yaƙi dan kalmar Allah ta zama maɗaukakiya, to shi ne sabo da Allah".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

An tambayi annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga saɓanin manufofin masu yin yaƙi; wanda ya yi yaƙi dan jarumtaka ko ƙabilanci ko dan aga matsayinsa a cikin mutane ko wanin hakan, wannene saboda Allah? Sai annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya yi yaƙi saboda Allah shi ne: Wanda ya yi yaƙi dan kalmar Allah ta zama ita ce maɗaukakiya.

فوائد الحديث

Asali a cikin gyaruwar ayyuka da ɓacinsu (ita ce) niyya da tsarkake aiki saboda Allah.

Idan manufa daga yaƙi ita ce ɗaukaka kalmar Allah, kuma wata manufar daban abar shara'antawa ta haɗu a cikinsa, kamar samun ganima, to shi ba ya cutarwa.

Kare maƙiya daga shiga garuruwa da mutuncin mata yana daga yaƙi saboda Allah.

Falalar da ta zo a cikin mayaƙa tana keɓantuwa ne ga wanda ya yi yaƙi dan kalmar Allah - Maɗaukakin sarki - ta zama ita ce maɗaukakiya.

التصنيفات

Ladaban Jihadi