Za'a samu babakere da wasu al'amuran da zaku kisu" suka ce : Ya Manzon Allah mezaka umarcemu? Ya ce: "Ku bada hakkin da ya wajaba akanku, kuma ku roki Allah hakkinku

Za'a samu babakere da wasu al'amuran da zaku kisu" suka ce : Ya Manzon Allah mezaka umarcemu? Ya ce: "Ku bada hakkin da ya wajaba akanku, kuma ku roki Allah hakkinku

Daga Dan Mas’ud - Allah ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Za'a samu babakere da wasu al'amuran da zaku kisu" suka ce : Ya Manzon Allah mezaka umarcemu? Ya ce: "Ku bada hakkin da ya wajaba akanku, kuma ku roki Allah hakkinku ".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wasu shugabanni zasu shugabanci musulmai, za su yi babakere da dukiyoyin musulmai da wasunsu daga al'amuran duniya, za su dinga juyasu kamar yadda suke so zasu hana musulmai hakkokinsu a dukiyar . Kuma wasu al'amuran da za'aki a Addini zasu kasance daga garesu. Sai sahabbai - Allah Ya yarda da su - suka yi tambaya: Me za su aikata a wannan halin? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ba su labarin cewa kada wawure (dukiya da suka yi) ya hanaku abinda ya wajaba akanku daura da su na ji da bi, kai ku yi hakuri ku ji ku bi , kada ku yi jayayya da su a al'amari, kuma ku roki Allah hakin dake gareku, kuma Ya gyrasu ya tunkude sharrinsu da zalincinsu.

فوائد الحديث

Hadisin yana daga alamomin Annabcinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - inda ya bada labarin abinda zai kasance a cikin al'ummarsa sai ya afku kamar yadda ya bada labari.

Halaccin sanar da wanda aka jarraba da abinda zai afku gareshi na bala'i; dan ya yi wa kansa tanadi idan ta zo masa, zai zama mai hakuri mai neman lada.

Riko da Alkur’ani da sunna mafitane daga fitintinu da sabani.

Kwadaitarwa akan ji da bi ga shugabanni da kyautatawa, da rashin tawaye garesu, koda zalinci ya afku daga garesu.

Anfani da hikima da bin sunna a lokaci fitintinu.

Ya wajaba ga mutum tsayuwa da hakkin dake kansa koda wani abu na zalinci ya faru akansa.

A cikinsa akwai dalili akan ka'idar: Ana zabin mafi saukin sharruka biyu ko mafi saukin cutuka biyu.

التصنيفات

Abubuwan da suka Wajaba kan Shugaba