: :

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Allah Ya turbuɗe hanacin, sannan Allah Ya turbuɗe hanacin, sannan Allah Ya turbuɗe hanacin" Aka ce: Wa ya Manzon Allah? Ya ce: "Wanda ya riski iyayen sa lokacin girma, ɗayan su ko su biyun amma bai shiga Aljanna ba".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya yi addu'a da ƙasƙanci da taɓewa har saida hakan ya kai, kai ka ce ya ɗora hancinsa a cikin ƙasa - ya maimaitata sau uku - sai aka tambaye shi: Waye wannan ya manzon Allah wanda ka yi mummunar Addu’a akansa? Sai (Annabi) tsira da a mincin Allah su tabbata aagre shi - ya ce: Wanda ya riski mahaifansa a lokacin tsufa - ɗayansu ko su biyun -, ba su zama sababi na shigarsa aljanna ba; hakan saboda rashin kyautata musu da kuma saɓa musu.

فوائد الحديث

Wajabcin biyayya ga mahaifa, kuma hakan yana daga sabubban shiga aljanna, musamman ma a lokacin tsufansu da rauninsu.

Saɓawa iyaye yana daga manyan zunubai.

التصنيفات

Falalar bin Iyaye