Allah Ya rubuta abinda ya kaddarawa halittu kafin Ya halicci sammai da kasa da shekara dubu hamsin

Allah Ya rubuta abinda ya kaddarawa halittu kafin Ya halicci sammai da kasa da shekara dubu hamsin

Daga Abdullahi dan Amr dan Amr dan Aas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Allah Ya rubuta abinda ya kaddarawa halittu kafin Ya halicci sammai da kasa da shekara dubu hamsin, ya ce: Al’ArshinSa yana kan ruwa".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa , Allah Ya rubuta abinda zai afku na abinda ya kaddarawa halittu a fayyace, na rayuwa da mutuwa da arziki da makamancin hakan a cikin Lauhul mahfuz , tun kafin ya halicci sammai da kasa da shekara dubu hamsin, abin yana afkuwane daidai da dacewar abinda Allah - mai girma da daukaka - Ya hukunta, Dukkanin wani abu mai kasancewa to da hukuncin Allah ne da ikonSa, Abinda ya samu bawa bai zama zai kuskure shi ba, abinda ya kuskure shi bai zama zai same shi ba.

فوائد الحديث

Wajabcin yin imani da hukunci da kaddara.

Kaddara ita ce : Sanin da Allah ya yi wa abubuwa da rubuta su da ganin damarSa da kuma halittar su da ya yi .

Imani da cewa kaddarori ababen rubutawane tun kafin halittar sammai da kasa yana haifar da yarda da mika wuya.

Lallai cewa Al’Arshin Ubangiji ya kasance akan ruwa tun kafin halittar sammai da kasa.

التصنيفات

Matakan Hukuncin Allah da Qaddara