Wanda ya manta wata sallah, to, ya sallaceta idan ya tunata, babu kaffara gareta sai hakan

Wanda ya manta wata sallah, to, ya sallaceta idan ya tunata, babu kaffara gareta sai hakan

Daga Anas Ɗan Malik Allah Ya yarda da shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Wanda ya manta wata sallah, to, ya sallaceta idan ya tunata, babu kaffara gareta sai hakan: {Ku tsai da sallah domin tunani} [Daha: 14".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayya cewa wanda ya mance yin kowacce sallar farilla har lokacinta ya fita, to, ya wajaba a kansa ya yi gaggawar ramata a duk lokacin da ya tunata, babu gogewa ko suturtawa ga laifin barinta sai dai kawai musulmi ya sallaceta a yayin da ya tunata, Allah Ya faɗa a littafinSa Mai girma: {Ka tsai da sallah domin tunaNi} [Daha: 14], wato: Ka tsai da sallar daka manta idan ka tunata.

فوائد الحديث

Bayanin muhimmancin sallah da rashin ko’unkula da yinta da kuma ramata.

Jinkirta sallah daga lokacinta da gangan ba tare da wani uzuri ba ba ya halatta.

Wajabcin rama sallah a kan mai mantuwa idan ya tuna, da mai bacci idan ya farka.

Wajabcin rama salloli a gaggauce ko da a lokutan hani ne.

التصنيفات

Wajabcin Sallah da Hukuncin wanda ya barta, Kusakuren Masu Sallah