إعدادات العرض
Kabar abinda kake kokwantansa, zuwa ga abinda baka kokwantansa
Kabar abinda kake kokwantansa, zuwa ga abinda baka kokwantansa
Daga Abu Muhammad al-Hasan ibnu Ali Ibnu Abi Ɗalib - jikan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma abin shinshinarsa -, ya ce: Na haddace daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: «Kabar abinda kake kokwantansa, zuwa ga abinda baka kokwantansa».
الترجمة
العربية Español አማርኛ English اردو Indonesia বাংলা Français Türkçe Русский Bosanski සිංහල हिन्दी 中文 فارسی Tiếng Việt Tagalog Kurdî Português മലയാളം తెలుగు Kiswahili தமிழ் ไทย Deutsch پښتو অসমীয়া Shqip Nederlands ગુજરાતી Кыргызча नेपाली Lietuvių دری Српски тоҷикӣ Kinyarwanda Română Magyar Čeština Moore Malagasy Oromoo ಕನ್ನಡ Wolof Azərbaycan O‘zbek Українська ქართული Македонски ភាសាខ្មែរ ਪੰਜਾਬੀ मराठी Kirundi Kurmancî Bahasa Melayu မြန်မာالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da barin abin da kake kokwanto akansa na maganganu da ayyuka cewa shin an hana kuwa ko a'a, shin haramun ne ko halal ne, zuwa ga abin da baka kokwanto a cikinsa daga abin da ka tabbatar da kyawunsa da kuma halaccinsa.فوائد الحديث
Ya wajaba akan musulmi ya gina al'amuransa akan yaƙini da barin abinda ake kokwanto a cikinsa, kuma ya zama mai basira akan Addininsa.
Hani daga afkawa cikin shubuhohi.
Idan kana son nutsuwa da hutu to kabar abinda ake kokwanto a cikinsa ka jefar da shi a gefe.
Rahamar Allah ga bayinSa, dan Ya umarcesu da abinda a cikinsa akwai hutun rai da zuciya, kuma ya hanesu daga abinda a cikinsa akwai raurawar zuciya da kuma ɗimuwa.
