Idan kun ji kiran sallah, to ku fadi irin abinda ladani yake fada

Idan kun ji kiran sallah, to ku fadi irin abinda ladani yake fada

Daga Abu Sa'id Al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan kun ji kiran sallah, to ku fadi irin abinda ladani yake fada".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kwadaitarwa akan amsa wa ladani a lokacin jinsa, hakan da mu fadi irin abinda yake fada, jumla da jumla, A yayin da ya yi kabbara sai mu yi kabbara a bayansa, a yayin da ya zo da shaida biyu, sai mu zo da su a bayansa. An togance lafazin: (Ku yi gaggawa zuwa sallah, ku yi gaggawa zuwa tsira) cewa za'a fada a bayansu: Babu dabara babu karfi sai ga Allah.

فوائد الحديث

Zai bi ladani na biyu bayan karewar na farko, koda ladanan suna da yawa; dan gamewar hadisin.

Ya amsawa ladani a kowanne hali, indai ba ya kasance ne a bayan gida ko yana kan biyan bukatarsa ba.

التصنيفات

Kiran Sallah da Iqama, Kiran Sallah da Iqama