Wanda ya sallaci sanyaya biyu zai shiga aljanna

Wanda ya sallaci sanyaya biyu zai shiga aljanna

Daga Abu Musa al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya sallaci sanyaya biyu zai shiga aljanna".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zaburar da kwaɗaitarwa akan sallar sanyaya biyu ; su ne sallar asuba da la'asar, kuma Ya yi wa wanda ya yi su da haƙƙinsu na lokaci da jama'a da wanin haka albishir cewa sun zama sababi na shigarsa aljanna.

فوائد الحديث

Falalar kulawa akan sallar asuba da la'asar; domin asuba tana kasancewa ne a lokacin daɗin bacci, la'asar kuma tana kasancewa ne lokacin shagaltuwar mutum da aikinsa, wanda ya kiyayesu ya kasance mafi cancanta ya kiyaye ragowar salloli.

An ambaci sallar asuba da la'asar da sanyaya biyu; domin sallar asuba a cikinta akwai sanyin dare, sallar la'asar kuma a cikinta akwai sanyin rana, koda sun kasance a lokaci na zafin rana, saidai wannan lokacin ya fi saukin (zafi) kafin wannan lokacin, ko kuma ambatansu ya zama ta babin rinjayarwa kamar yadda ake cewa: Watanni biyu ga rana da wata.

التصنيفات

Falalar Sallah